Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano - Anti-Phone Snatching Force

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force da ke nan Kano, ta ce ta hanyar daƙile sha da dillancin miyagun ƙwayoyi ne za a kawar da harkokin faɗan daba, da ƙwacen waya a sassan jihar nan, tare da samun zaman lafiya.
Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ne ya sanar da hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, lokacin da yake tsokaci kan shirin rundunar na ƙara shiri wajen daƙile ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Nura Salisu Sharaɗa ya kuma ce a kullum aikin da suke yi shi ne bibiyar wuraren da ake dillanci miyagun ƙwayoyi, inda ya ce babu ɗaga ƙafa tsakanin su da dillallan kwayoyi matuƙar suka kama su, kamar yadda Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya umarce su akai.
A cewar sa, "Yanzu haka mun ƙara baza jami'an mu a lungu da saƙo na jihar Kano, domin farauto masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyin, da kuma masu tada hankalin al'umma ta hanyar faɗa daba, da ƙwacen waya," in ji Nura.
Ya kuma gargaɗi dukkanin masu ta'ammali da kayan maye da su daina su canza sana'a yana mai cewa duk mutumin da suka kama da wannan laifi ba za su ɗaga masa ƙafa ba ko waye, har ma da masu goya musu baya.



