Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama mutane 7 kan zargin su da sha da dillancin kayan maye a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta kama mutane bakwai a filin wasa na Mahaha, bisa zargin su da sha da dillancin kayan maye da ke bugarwa.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya sanar da hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Laraba 29 ga Yuli, 2026.
Ya ce bayan samun rahoton sirri ne kan yadda ake hada-hadar ƙwayoyi da dillancin sauran kayan maye a wasu ɓangarori na cikin filin wasa na Mahaha, kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya umarce jami'an sa ƙarkashin jagorancin DC Abduljalal Sa'id Muhammad, suka halarci wajen.
"Lokacin da jami'an mu suka je wajen sun tarar da yadda ake hada-hadar ƙwayoyi da Madarar Sukudayin da Sholisho, inda suka farmake su, masu tarin kayan mayen suka tsere, sai dai sun kama mutane 7 da suka je sayen kayan maye," in ji shi.
Ibrahim Garba Ahmad ya ƙara da cewa, wannan na zuwa ne a ci gaba da faɗaɗa sintirin su na shiga lungu da saƙo na jihar Kano, wajen zaƙulo masu sha da dillancin kayan maye, a salon aikin nan nasu na "Damisa Ƙi Sabo" domin ɗaukar mataki a kan duk wanda aka kama da wannan laifi.
Da suke jawaban su daban-daban, mutanen da ake zargin sun bayyana nadamar su bisa yadda aka kama su lokacin da suka je sayen kayan mayen a filin wasa na Mahaha da ke Ƙofar Na'isa a Kano.
Ya ce bayan da suka kama mutanen bakwai ne Kwamandan rundunar ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, Nura Salisu Sharaɗa ya yi umarni aka kai mutanen ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano.
Nura Salisu Sharaɗa ya kuma gargaɗi ɓata garin da suke addabar jama'a da harkokin faɗan daba, da ƙwacen waya da shaye-shayen kayan maye, da su daina kasancewar duk wanda ya zo hannun su na zai ji da daɗi ba.



