NASENI ta ƙaddamar da rabon kayan aiki ga mata 50 a Kano, bayan basu horo a kan gyaran Solar

Hukumar inganta harkokin kimiyya da fasaha ta ƙasa NASENI, ta ƙaddamar da rabon kayan aiki ga mata 50 a jihar Kano, bayan basu horon kwanaki uku a kan gyaran Solar.
Shugaban hukumar Mallam Khalil Sulaiman Halilu, ya bayyana cewar sun ɗauki matakin koyawa mata gyaran solar ne saboda ana barin su a baya a irin waɗannan abubuwa.
Halilu ya kuma ce sun baiwa matan kayayyakin gyaran solar domin inganta rayuwar al'ummar, domin ilmantar da mata tamkar ilmantar da al'umma ne.
Waɗanda da suka ci gajiyar tsarin da yawancin su suka kasance ƴan mata sun bayyana cewar za su rungumi aikin hannu bibbiyu, biyo bayan horon da suka samu.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, taron ya gudana ne a Kano, inda ƴan uwa da abokan arziki na matan sun bayyana godiyarsu ga hukumar ta NASENI, bisa horon da ta baiwa ƴan uwan su.



