Ƴan daba sun kai wa ayarin motocin Kwankwaso da Aminu Gwarzo hari a Kano.

Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, yayin ziyarar yaƙin neman zaɓe a ƙaramar hukumar Bichi.
Kafar Daily Trust ta ruwaito cewa Mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan, Comrade Ibrahim Garba Shu’aibu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamba, 2026.
Ya ce wasu matasa ɗauke da makamai sun tare ayarin motocin tare da far wa tawagar.
Ya bayyana cewa harin ya jikkata wasu mambobin tawagar, tare da lalata motoci kusan bakwai. A cewarsa, tawagar ta gudanar da yakin neman zaɓe cikin nasara a wasu ƙananan hukumomi shida kafin ta isa Bichi, inda lamarin ya faru.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kano ba ta fitar da sanarwa kan harin ba.



