Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snaching force ta kama Aminu Muhammad kan zargin yunƙurin kashe mahaifiyarsa a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 1 views
Rundunar Anti-Phone Snaching force ta kama Aminu Muhammad kan zargin yunƙurin kashe mahaifiyarsa a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da daƙile sha da dillancin miyagun ƙwayoyi ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force a Kano, ta cafke matashi Aminu Muhammad, bisa zargin sa da yunƙurin kashe mahaifiyar sa a unguwar Burget.

Mai magana da yawun rundunar tsaron, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana wa Dala FM Kano, kama matashin a ranar Litinin 12 ga watan Oktoba, 2026.

A cewar sa, matashin mai suna Aminu Muhammad mai shekaru 21, mazaunin unguwar Burget a Kano, an yi zargin ya bi mahaifiyar sa a cikin gida ɗauke da wuƙa, inda ya yi yunƙurin kashe mahaifiyar tasa.

Ya ce bayan da suka samu rahoto a kan matashin ne, kwamandan rundunar Nura Salisu Sharada, ya tura jami'an sa na "Operation Damisa Ƙi Sabo" inda suka zabaro matashin tare da kawo shi hedikwatar rundunar da ke unguwar Sharaɗa.

Ibrahim Garba ya ce binciken su na farko ya gano cewa, matashin ya yi yinƙurin kashe mahaifiyar tasa ne sakamakon ƙwayar da yasha da ake kira Fiji.

Ya ce sun ci gaba da gudanar da bincike a kan matashin kuma da zarar sun kammala za a miƙa shi inda ya dace domin ɗaukar mataki na gaba.

Da yake zantawa da Dala FM Kano, matashi Aminu Muhammad, ya ce ƙwayar da ya sha ce ta sanya shi yunƙurin kashe mahaifiyar sa, lamarin da ya ce ya tayar masa da hankali.

Ya kuma ce yana shan ƙwaya samfurin Fiji, da wani nau'in kayan shaye-shaye da ake kira da Ice, duk kuwa da lalurar ƙafa da yake ɗauke da ita (Gurgu).

Matashin ya kuma bayyana nadamar sa, inda ya ce da yardar Allah daga yanzu ya daina shan kayan mayen tunda dai ba sa haifar masa da ɗa mai ido.

Daga bisani Kakakin rundunar, Ibrahim Garba, ya kuma gargaɗi matasabda da su gujewa aikata laifuka kasancewar duk wanda ya faɗa hannun su ba za su saurara masa ba.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM