NDLEA ta kama mutane 80, ta tarwatsa guraren da ake ta'ammali da kayan maye guda 16 a Kano.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta lasa (NDLEA), reshen jiha Kano, ta kama mutane 80, da ake zargi da ta'ammali da kayan maye, tare da tarwatsa wasu fitattun wuraren da ake safarar da kuma shan miyagun ƙwayoyi guda 16 a jihar.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar ACN Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya sanar hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Talata 18 ga watan Agusta, 2026.
Ya ce hukumar ta kama mutanen ne a cikin kwanaki bakwai, biyo bayan umarnin da suka samu daga babban jami'in hukumar su na ƙasa, Burgediya Janar Muhammad Buba Mai Ritaya, na tabbatar da cewa an tarwatsa duk wata matattara da ake amfani da ita wajen ta'ammali da kayan maye.
A cewar sa "Bayan samun wannan umarni ne Babban jami'in hukumar ta NDLEA, a Kano, Ɗahiru Yahaya Lawan, ya tashi jami'an hukumar inda suka shiga lungu da saƙo suka farauto mutane 80, tare da tarwatsa mafakar masu ta'ammali da kayan maye guda 16 a sassan jihar," in ji Sadiq.
Ya ce hukumar ta kai sumamen ne unguwannin Filin Mahaha, Unguwar Ƙoƙi, da Ɗorayi, Chiranchi, Rijiyar Lemo, Kasuwar Kurmi, Wambai, da Sauna, da dai sauran wasu gurare a sassan jihar Kano.
Ya kuma ce hukumar ta ƙwace kayayyaki kala kala a wajen mutanen da suka haɗar da Tabar Wiwi, da Ƙwayar Tramadol, Freegabling, Exol, wacce ake yi wa laƙabi da sha fara ka ga aljan, da Arungumo Zaki, da dai sauran su.
ACN Sadiq Muhammad Maigatari ya kuma ce da zarar an kammala bincike a kan mutanen za a ɗauki matakin da ya dace a kan su.
A cewar sa, "Wannan sumame zai ci gaba da gudana a sassa daban-daban na jihar Kano, har sai masu ta'ammali da kayan mayen sun rasa wajen sha da sayarwa a jihar Kano," in ji Maigatari.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin a Kano, ta kuma buƙaci dukkan masu ta'ammali da kayan maye da su tuba su daina tun kafin lokaci ya ƙure musu, domin ba za ta saurara wa dukkan wanda ta kamata ba.



