Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta fara rarraba ruwan Famfo daga rumbun ajiya na Goron dutse bayan shekaru 30 baya aiki.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta fara rarraba ruwan Famfo daga rumbun ajiya na Goron dutse bayan shekaru 30 baya aiki.

Gwamnatin Kano ta ce tana dab da fara tura ruwan sha na famfo sama da lita miliyan 40 ga al’ummar ƙwaryar birnin jihar, a yunƙurin ta na kawo karshen matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar mazauna jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara domin duba yadda aikin gyaran rumbun ajiyar ruwa na Goron Dutse yake gudana.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM