Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da fara tura ruwan sha lita miliyan 40 kullum a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da fara tura ruwan sha lita miliyan 40 kullum a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da fara tura ruwan sha sama da lita miliyan arba'in da zai shiga ko ina a kwayar birnin Kano.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya ƙaddamar da fara tura ruwan a yau, domin al'ummar jihar su sami sauƙin wahalar ruwa da aka sha a watannin baya a Kano.

Idan ba za a manta ba tun a watan Afrilun na shekarar 2026, ne al'ummar Kano suka dinga shan wahalar ruwa kuma a lokacin gwamnan ya sha alwashin samar da ruwan shan.

Gwamnan ya dai bayyana ware sama da biliyan goma sha ɗaya domin samar da ruwan kamar yadda aka yi a yanzu.

An dai gudanar da aikin ne ta karkashin kwamishina ruwa da muhalli da kuma sauyin yanayi Dr. Ɗahir Muhammad Hashim, inda aka ba wa wani kamfani da ke da ƙwarewa a Duniya don ganin an yi aiki mai inganci.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM