Talakawa ne suka fi shan wahala a ƙasar da cin hanci ya yi mata dabaibayi - Obasanjo
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce cin hanci da rashawa da kuma dukiyar da ba a san tushenta ba na kawo cikas ga ci-gaban ƙasa.
Obasanjo ya ce talakawa ne suka fi shan wahala a cikin al’ummar da cin hanci ya yi ƙarfi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obasanjo ya ce, tun lokacin da yake aikin soja yake yaƙi da cin hanci.
A cewar sa, ya taɓa zama mai gabatar da ƙara a ƙarƙashin dokokin soja tare da shiga kotun soji da ta binciki wasu laifukan cin hanci da rashawa.



