Koma Labarai
Masarauta

Masarautar Kano ta dakatar da Dagacin Rikadawa kan zargin sayar da Gonakin Hakimi babu izinin sa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Masarautar Kano ta dakatar da Dagacin Rikadawa kan zargin sayar da Gonakin Hakimi babu izinin sa

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya dakatar da Dagacin garin Rikadawa da ke ƙaramar hukumar Madobi, Malam Rabi’u Yusuf, bisa zargin sa da laifi.

An bayyana hakan ne ta bakin Matawallen Kano, Alhaji Ali Ibrahim Ahmad Matawalle, da Wazirin Kano, Alhaji Sa’ad Shehu Gidado, yayin da suke sauraron korafin wasu al’umma da ke zargin yaron hakimi, Isah Dahiru, da Dagacin garin Rikadawa da sayar da gonakin Hakimin ƙaramar hukumar Madobi, Alhaji Sale Musa Kwankwaso, ba tare da sanin sa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu Dagacin da hannu cikin wannan badaƙalar sayar da gonakin Hakimin, abin da suka bayyana a matsayin cin amanar Masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, ɗaya daga cikin masu korafin, Muddasir Ɗahiru, ya ce ya shigar da ƙorafi ne gaban Sarkin Kano, bisa zargin cin amanar da yaron hakimi da Dagacin garin Rikadawa suka yi masa na sayar da gonakin Hakimin ƙaramar hukumar Madobi ba tare da saninsa ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM