Koma Labarai
Masarauta

Sarkin Kano ya amince da murabus ɗin dagacin garin Gundurwa da ke ƙaramar hukumar Munjibir Mallam Garba Ahmad.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Kano ya amince da murabus ɗin dagacin garin Gundurwa da ke ƙaramar hukumar Munjibir Mallam Garba Ahmad.

‎‎Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya amince da murabus ɗin Dagacin Garin Gundurwa da ke ƙaramar hukumar Minjibir, Malam Garba Ahmad, bisa rashin lafiyar da take damun sa.

‎Sarkin ya aminta da murabus ɗin ne ta bakin Wazirin Kano Alhaji Sa'ad Shehu Gidado yayin zaman majalisar ranar Laraba 22 ga Yuli, 2026.

Da yake jawabi Wazirin Kano Alhaji Sa'ad Shehu Gidado, ya ce bisa al'adar masarautar Kano dagacin ba shi da hurumin neman kawo wanda zai gaje shi sai abin da masarautar ta shirya, inda ‎ya kuma umarci da akai dagacin ofis domin shirya masa takardun yin murabus ɗin.

A nasa ɓangaren ‎Malam Garba Ahmad, ya ce ya ajiye aikin dagacin garin Gundurwa ne bisa dalilan rashin lafiya da yake fama da ita, da kuma daina sauraron korafe-korafen al'ummar garin.

‎‎Wakilinmu na masarautar Kano Shu'aibu Ubale Minshawi ya rawaito cewa, a yayin zaman majalisar masarautar ta Kano, na yau Laraba, masu korafe korafe sun gabatar da kokensu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM