Sarkin Kano Sanusi, ya yaba da tsare-tsaren Aliko Ɗangote, kan kawo cigaban tattalin arziƙi a jihar.

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya yaba da tsare tsaren shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, kan kawo cigaban tattalin arziki a jihar, da ma ƙasa baki ɗaya ta fuskar harkokin kasuwanci.
Sarkin ya yi wannan yabo ne yayin taron ƙaddamar da hannun jari da Alhaji Aliko Ɗangote ya yi a nan Kano, domin amfanin al'ummar jihar na sayen hannun jari.
Khalifa Muhammad Sanusi na biyu ya kuma bayyana Kano, a matsayin cibiyar Kasuwanci da tafi ko ina a Afrika, a don haka ya yi kira ga al'umma da su yi amfani da damar wajen samun cigaban a harkokin Kasuwanci.
A nasa jawabin, Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Alhaji Aliko Ɗangote, ya yi kira ga al'umma da su shiga cikin tsarin na Ɗangote domin ƙara haɓaka harkokin kasuwanci da kuma samun gwaggwaɓar riba.
A yayin taron, Babban limamin Masallacin juma'a na Al-furƙan Dakta Bashir Aliyu Umar, ya yi jawabi mai tsawo a kan yadda al'ummar za su sayi hannun jari ta hanya mai sauƙi ba tare da wasu sun wahalar da su ba.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, daga cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tajo Aminu Ɗantata, AB Mahmud, Alhaji Sabi'u Baƙo, Dakta Farouk Umar, sai Mista Tilewa Adebajo, da kuma manyan ƴan kasuwar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.



