Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II ya miƙawa Hakimai biyu motocin da Hon. Kawu Sumaila ya basu kyauta.

Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya yaba da ƙoƙarin Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, bisa kyautar motoci guda biyu da ya baiwa Hakimin Sumaila, da na gundumar Rimi, domin sauƙaƙa musu wajen gudanar da ayyukansu.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake miƙa motocin ga hakimin Sumaila, kuma Galadiman Daji Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi, da takwaransa na Gundumar Rimi, kuma Sarkin Sulluɓawan Kano Alhaji Idris Sanusi Bayero a fadarsa.
Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana wannan mataki a matsayin ci gaba mai kyau, yana mai cewa motocin za su taimaka matuƙa wajen sauƙaƙawa hakiman gudanar da ayyukan da aka ɗora musu na jagorantar al’ummar yankin sumaila.
A nasu ɓangaren hakimin Sumaila Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi, da hakimin Gundumar Rimi, kuma Sarkin Sullubawan Kano Alhaji Idris Sanusi Bayero, sun godewa Sanata Kawu Sumaila bisa wannan karamci da ya yi musu na basu kyautar motocin.
Sun kuma jaddada aniyarsu ta cigaba da tallafa wa duk wani yunƙuri da zai kawo cigaba ga ƙaramar hukumar Sumaila, da Masarautar Kano baki ɗaya.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, Mai Martaba ya kuma yi kira ga sauran shugabannin siyasa da su yi koyi da irin wannan kyakkyawan aiki, domin tallafa wa shugabannin gargajiya da kuma ƙara samar da cigaba a yankunan su.



