Koma Labarai
Masarauta

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kammala Hawan Sallar Gani a jihar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kammala Hawan Sallar Gani a jihar.

‎Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya kammala hawan sallar gani na kwanaki biyu, inda ya kewaya sassa daban-daban na birnin Kano, domin nuna murnar bukukuwan maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.

‎Sarkin ya shirya wannan hawa ne domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu S.A.W, wanda ya kasance karo na farko a tarihin Masarautar Kano.

An gudanar da hawan sallar gani, ne a ranakun Asabar 29, da Lahadi 30 ga watan Agusta, 2026.

‎Hawan a bana ya samu halartar manyan mutane da kuma dandazon matasa maza da mata da tsofaffi, waɗanda suka fito domin nuna farin cikinsu ga Mai Martaba Sarkin na Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, bisa hawan da ya jagoranta.

‎Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, a yayin hawan Mai Martaba sarkin ya cigaba da yi wa al’umma addu’o’i, musamman na zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Kano da Najeriya baki ɗaya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM