Koma Labarai
Masarauta

Sarkin Kano Sanusi II, ya buƙaci ƴan kasuwa su karɓi tsarin inshorar muslunci don sauƙaƙawa kasuwancin su a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Kano Sanusi II, ya buƙaci ƴan kasuwa su karɓi tsarin inshorar muslunci don sauƙaƙawa kasuwancin su a Kano

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci ƴan kasuwa da su karɓi tsarin inshorar muslunci domin sauƙaƙawa harkokin kasuwancin su a jihar nan da ma ƙasa baki ɗaya.

‎Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci taron ƙaddamar da asusun  Afrinvest wanda aka gudanar yau Alhamis a nan Kano.

‎Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya ce, jihar Kano jiha ce da ta shahara a harkokin kasuwanci a afrika, a don haka akwai buƙatar ƴan kasuwa su rungume inshorar muslunci domin ƙara bunƙasa harkokin kasuwancin su, ciki har da lokacin da aka samu wani iftila'i.

Har ila yau, sarkin ya kuma jagoranci buɗe Cibiyar gudanar da jarabawa ta ICT, da aka buɗe yau a masarautar Kano.

‎A nasa jawabin, shugaban cibiyar Dakta Ike Chioke, ya ce an samar da cibiyar a masarautar Kano ne domin zai taimakawa ɗalibai samun saukin zana jarabar Jamb, ya kuma bayyana farin cikin sa bisa yadda mai martaba Sarkin ya bude Cibiyar da kansa.

‎Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, a yayin bikin buɗe Cibiyar, sarkin yana tare da wasu daga cikin hakimansa, ciki har da Galadiman Kano, da Wazirin Kano, da kuma Madakin Kano, sai Matawallen Kano da dai sauransu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM