Koma Labarai
Masarauta

Rushewar Gidaje 124: Gwamnatin Kano a tallafawa mutanen da Iftila'in ya shafa a Magami - Sarkin Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rushewar Gidaje 124: Gwamnatin Kano a tallafawa mutanen da Iftila'in ya shafa a Magami - Sarkin Kano

Mai Martata sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya jajanta wa mazauna garin Magami da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila, bisa yadda iftila'in iska da ruwan sama mai ƙarfi suka haifar da rushewar gidaje da yayewar kwanukan rufin gidaje 124 a yankin su.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da Dagacin Magami, Mallam Nura Ahmad, ya jagoranci al'ummar yankin domin kai masa rahoton faruwar Iftila'in a ranar Litinin 13 ga Yuli, 2026.

Khalifan Muhammadu Sanusi II, ya kuma bukaci mutanen da su mayar da lamuran su ga Allah Madaukakin sarki, tare da addu'ar ya mayar musu da mafificin alkhairi.

Sarkin ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kai wa waɗanda ifitila'in ya faru da su tallafin gaggawa, domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Wakilinmu na masarautar Kano Shu'aibu Ubale Minshawi ya rawaito cewa, Dagacin na garin Magami Mallam Nura Ahmad, ya tabbatar wa sarkin cewa, iftila'in ya haifar da rushewar gidaje da cirewar rufin dakuna guda 124, amma dai ba a sami asarar rayuka ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM