Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya dakatar da Dagacin Garin Badawa Zakari Ya'u, bisa zargin cin amana a harkar filaye

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya dakatar da Dagacin Garin Badawa da ke karamar hukumar Nasarawa, Alhaji Zakari Yau, bisa zargin cin amana da ta shafi filaye.
Sarkin ya dakatar da dagacin ne a ranar Talata 28 ga Yuli, 2026, inda ya bayyana cewa, dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an kammala binciken da Masarautar Kano ke gudanarwa kan zargin da ake masa.
Tun da farko, wasu daga cikin mazauna unguwar Badawa ne suka gabatar da korafinsu a gaban Hakimin yankin, daga bisani kuma aka miƙa lamarin zuwa gaban Mai Martaba Sarkin Kano, domin gudanar da cikakken bincike.
Wakilinmu na fadar masarautar Kano Shu'aibu Ubale Minshawi ya ruwaito cewa, bayan sauraron bayanan ɓangarorin da abin ya shafa, Mai Martaba Sarkin ya amince da dakatar da Dagacin daga muƙaminsa na wucin gadi, har zuwa lokacin da za a kammala bincike tare da daukar matakin da ya dace kan sakamakon binciken.



