Sarkin Kano ya amince da murabus ɗin dagacin garin Rugu-rugu Mallam Bello Muhammad

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na II, ya amince da yin murabus ɗin dagacin garin Rugu-rugu da ke Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, Malam Bello Muhammad, mai shekaru 85, sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.
A ranar Laraba 8 ga Yuli, 2026, Dagacin ya shaidawa sarkin cewa, shi ne da kansa yake son yin murabus ɗin ba tare da an tilasta shi ba, saboda yanzu tsufa ya kama shi ba zai iya aikin ba.
Mai martaba Sarkin ta bakin Babban ɗan majalisar sarki, Matawallen Kano Alhaji Aliyu Ibrahim, ya ce an amince da yin murabus ɗin Dagacin, amma da sharaɗin ba zai kawo wanda za a naɗa a matsayin sabon dagacin ba, sai wanda mai martaba sarki ya amince da shi.
Dagacin mai shirin yin murabus ya ce ya amince da sharaɗin Sarkin, haka kuma masarautar Kano ta bada damar a shirya yi masa ritaya.
A nasa jawabin Malam Sani Bello ɗa ga dagacin mai shirin yin murabus, ya ce sun godewa masarautar Kano, da ta amince da yin murabus ɗin mahaifin nasu.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, majalisar masarautar Kano ta kuma karɓi rahotan kisan wani mutum da aka yi a garin mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanbatta.



