Sanata Rufa'i Hanga bai fice daga NDC zuwa APC ba - Samir Hanga
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Guda daga cikin ƴaƴan Sanatan Kano ta tsakiya, Rufa'i Sani Hanga, wato Samir Rufai Hanga, ya musanta rahotannin da ke yawo yana cewa mahaifinsa ya fice daga jam'iyyar NDC Kwankwasiyya zuwa APC.
Cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na Facebook, a yau, Samir ya ce har yanzu Sanata Hanga bai sanar da su a hukumance cewa ya bar jam'iyyar NDC ba.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa kan lamarin, kuma duk wani matsayi na ƙarshe za a ji shi ne daga bakin Sanata Hanga da kansa.
Ya bukaci jama'a da su yi hattara da rahotannin da ba su da tabbaci, inda ya kuma yi wa kowa fatan alheri.



