Isma'il Salisu ya yi watsi da dakatarwar da Majalisar Kansilolin Gwarzo, ta yi masa daga Kansilan Mazaɓar Unguwar Tudu.

Zaɓaɓɓen Kansilan Mazaɓar Unguwar Tudu da ke ƙaramar hukumar Gwarzo, Barista Isma'il Salisu, ya yi watsi da batun dakatarwar da Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar ta yi masa.
Barista Isma'il Salisu Gwarzo, ya bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da ya aiko wa Dala FM Kano, a cikin daren Alhamis 17 ga watan Satumba, 2026.
A yau Alhamis ne dai Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar Gwarzo, ta bayyana dakatar da Isma'il Salisu, bisa zargin rashin biyayya ga tsaron shugabanci, da kuma yi wa Gwamnatin Kano zagon ƙasa, da kuma kawo wa Gwamnatin cikas a ayyukan ta.
Sai dai, Barista Isma'il Salisu, ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa, inda ya ce basu da tushe ballantana makama.
A cewar sa, "Na lura da cewa waɗanda suka zauna suka bayyana dakatar da ni an basu umarni ne kawai, amma su kan su sun san cewa ban aikata laifukan da ake zargina a kan su ba," in ji shi.
Isma'il Salisu ya yi zargin cewa, an ɗauki matakin dakatar da shi ne sakamakon yadda yake ɗan jam'iyyar NDC, tare da biyayya ga tsarin Kwankwasiyya.
Ya kuma ce har yanzu shi ɗan jam'iyyar NDC, ne, sannan zai ci gaba da biyayya ga tafiyar jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma Ɗan takarar Gwamnan Kano, a jam'iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdulssalam Gwarzo.
Barista Isma'il ya kuma ƙara da cewa, babu wani zargi da Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar Gwarzo, ta taɓa tuhumar sa da shi, kuma ba ta taɓa rubuta masa wata takarda ta gargaɗi da cewar ya yi wani laifi ba.
A cewar sa, akwai lokuta da dama shi ne ma yake nusar da Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar, da su rinƙa zama, ko kuma ya nemi cewar a zo a zauna domin a duba al'ummar ƙaramar hukumar.
Ya ci gaba da cewa, "Babu wani zaman Majalisar ƙaramar Hukumar da aka yi ba tare da shi ba, amma abin mamaki aka umarci dakatar da shi, inda ya jaddada watsi da dakatarwar".
Isma'il ya kuma ce babban burin sa shi ne, Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma Kwamared Aminu Abdulssalam Gwarzo, da sauran ƴan takarar su na jam'iyyar NDC, su yi nasara a zaɓen 2027, da ke tafe.



