Sanata Rufa'i Sani Hanga ya fice daga jam'iyyar NDC a hukumance

Sanatan Kano ta tsakiya, kuma mataimakin mai tsawatar da marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Rufai Sani Hanga, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NDC, a hukumance.
A cikin wasiƙar murabus ɗin sa mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam'iyyar na mazabar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, Hanga ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki ne nan take.
Hanga ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari da tunani mai zurfi, yana mai cewa ya bar jam'iyyar ne domin mayar da hankali kan wasu al'amuran rayuwarsa da kuma ci gaban aikinsa.
Sanatan ya kuma miƙa godiyarsa ga shugabannin jam'iyyar a matakin mazaɓa, da kwamitin gudanarwa da daukacin mambobin NDC bisa irin goyon baya, dama da haɗin kai da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
Har ila yau, Sanata Hanga ya kuma buƙaci a cire sunansa daga kundin rajistar mambobin jam'iyyar a matakin mazaɓa, tare da bayyana cewa ya mayar da katin shaidar zama ɗan jam'iyyar NDC.
Sanatan ya yi wa jam'iyyar da mambobinta fatan alheri da nasara a dukkan ayyukansu na gaba, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.
Sai dai, a cikin wasiƙar murabus ɗin, Sanata Hanga bai bayyana ko yana da shirin komawa wata jam'iyyar siyasa ba a Najeriya.



