Koma Labarai
Siyasa

"Tinubu Must Go" Yaudara ce da aka karɓo kwangilar ta kuma ba za ta ɓulle ba - Amb. Ƙaribu Kabara

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
"Tinubu Must Go" Yaudara ce da aka karɓo kwangilar ta kuma ba za ta ɓulle ba - Amb. Ƙaribu Kabara

Ɗan gwagwarmaya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Ambasada Karibu Yahaya Lawal Kabara, ya ƙalubalanci jagororin tawagar "Tinubu Must Go" a Najeriya.

Ambasada Karibu Kabara ya bayyana haka ne a shafin sa na sada zumunta, ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2026.

A ƴan kwanakin nan ne dai Lauyan nan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Abba Hikima Fagge, aka hango su sun fito da aƙidar "Tinubu Must Go" ko da ike daga baya an hango wasu na bayyana "Tinubu Must Stay".

Sai dai Ƙaribu Kabara ya ce, duk waɗanda suke bayyana aƙidar "Tinubu Must Go" suna yi ne domin cimma muradan su wajen samun kuɗi da kuma son rai.

Ambasada Karibu Kabara, ya kuma zargi masu tallata "Tinubu Must Go" da cewar sun karɓo kwangila ne kawai daga ƴan adawa, ba wai don kishin Najeriya ba.

A cewar sa, "Waɗanda suka karɓo kwangilar "Tinubu Must Go" sun karɓo ne kawai domin aljihun su, da kuma son zuciya da kuma son a basu kujera, amma ba don kishin al'umma ba,"in ji Ƙaribu.

Kabara, wanda shi ne Babban Daraktan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network a Najeriya, ya kuma ce masu bayyana "Tinubu Must Go" idan siyasa suke son yi kamata ya yi su tsaya takara domin a dama da su, ba wai karɓo kwangila don aljihun su ba.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya kawo ƙarshen duk wata masifa da ke damun al'umma a Najeriya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM