Ɗan takarar Gwamnan Kano a jam'iyyar Youth Party da tawagarsa sun fice daga jam'iyyar

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Youth Party (YP), Kwamared Auwal Usman Awareness, ya jagoranci wani gagarumin taron siyasa da ya haɗa ’yan takara da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban na Jihar Kano.
Taron ya da ya gudana a yankin gidan Zoo a Kano, ya samu halartar ’yan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kano guda 40, da ’yan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya guda 24, sai ’yan takarar Sanata guda 3, tare da dimbin magoya bayan jam’iyyar daga gurare daban-daban.
Bayan kammala taron, Kwamared Auwal Usman (Awareness) ya bayyana cewa, shi da tawagarsa sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar Youth Party (YP), bisa wasu dalilai da ya bayyana yayin taron.
Ya ce sun shirya tsaf wajen tunkarar zaɓen 2027, da ke tafe, yana mai cewa lokaci ya wuce da shugabanni za su rinƙa zaluntar jama'a, da kuma murɗe zaɓe.
Awareness ya kuma yi kira ga magoya bayansu da ke faɗin Jihar Kano, da su ci gaba da kasancewa tare da su, tare da bibiyar matakan da za su ɗauka wajen tantancewa da zaɓen wata jam’iyyar siyasa da za su mara wa baya a babban zaɓen shekarar 2027.
Auwal Usman ya bayyana cewa ba za su yi gaggawar komawa wata jam’iyya ba, sai sun yi nazari tare da tuntubar magoya bayansu, domin tabbatar da cewa jam’iyyar da za su koma ita ce wadda za ta dace da manufofinsu da burinsu na siyasa.
A yayin jawabin nasa, Auwal Usman ya kuma bayyana godiyarsa da matuƙar farin cikinsa ga ɗaukacin magoya bayansu da suka halarci taron, inda ya yaba da yadda suka nuna haɗin kai, jajircewa da goyon baya.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa, haɗin kai da bin sahun tafiyar, yayin da ake ci gaba da tuntubar juna domin yanke shawarar mataki na gaba.
Ya kuma buƙaci gwamnatin jihar Kano, da ta daina yaudarar mutane, ta mayar da hankali wajen samar da ci gaban al'ummar jihar.



