Sanata Rufa'i Sani Hanga ya bar Jam'iyyar NDC Kwankwasiyya, ya koma APC
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatan Kano ta Tsakiya Alhaji Rufa'i Sani Hanga, ya fice daga jam'iyyarsa ta NDC Kwankwasiyya, ya koma APC.
Sanata Rufa'i Hanga ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da Nasir Salisu Zango a yau Alhamis 30 ga Yuli , 2026, inda ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa raɗin kansa da kuma nema wa kansa mutunci da kima a siyasance.
Wannan na zuwa ne tun bayan rasa takarar Sanatan da yake kai ta Kano ta tsakiya, da kuma aiwatar da wasu hukunce-hukunce a jam'iyyar ba tare da neman izininsa ba.



