Koma Labarai
Labarai

Musulman Najeriya ku ƙara haɗa kan ku - Sarkin Musulmi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Musulman Najeriya ku ƙara haɗa kan ku - Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al'ummar Musulmai da su ƙara haɗin kai tare da kare ’yancinsu wajen gudanar da addini ba tare da tsangwama ba.

Sarkin ya buƙaci hakan ne a wajen babban taron majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta ƙasa (NSCIA), wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, 2026.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na uku, ya kuma ce taron ya kasance muhimmi, musamman wajen ganin cewa shekaru kusan bakwai kenan tun bayan gudanar da irin wannan babban taro na majalisar.

Alhaji Sa'ad Abubakar ya kuma buƙaci shugabannin musulmi da su yi amfani da damar wajen musayar ra’ayoyi da ƙarfafa zumunci a tsakaninsu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM