Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta bayar da kwangiloli da suka haura biliyan 27, don gina cibiyoyin ICT, da CBT a jihar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta bayar da kwangiloli da suka haura biliyan 27, don gina cibiyoyin ICT, da CBT a jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da kwangiloli da darajarsu ta kai Naira biliyan 27,806,392,540 domin gina cibiyoyin Fasahar Sadarwa da Kwamfuta (ICT) da kuma (CBT) a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar nan.

Bayanin Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami'n hulda da jama'a na ma'aikatar kananan hukumomi na jihar Kano, Aminu Sani Bello ya fitar a ranar Talata 19 Agusta, 2026.

Sanarwar ta ce manufar yin hakan shi ne domin faɗaɗa damar samun ilimin zamani na dijital, domin gudanar da jarabawa ta hanyar kwamfuta, da kuma koyar da matasa dabarun amfani da fasaha a matakin ƙananan hukumomin jihar Kano.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, kwamishinan ƙananan hukumomi da Harkokin Masarautu na jihar Kano, Mohammed Tajo Othman, ya ce, aikin na matsayin wani muhimmin tarihi a faɗin jihar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM