Koma Labarai
Tsaro

Limaman masallatan juma'a ku yi addu'ar samun zaman lafiya a Tsanyawa da Kano, a huɗubobin ku - Hikimin Tsanyawa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Limaman masallatan juma'a ku yi addu'ar samun zaman lafiya a Tsanyawa da Kano, a huɗubobin ku - Hikimin Tsanyawa

Hakimin Tsanyawa, kuma Kaigaman Kano, Alhaji Ado Abdullahi Aminu, ya buƙaci dukkannin Dagatai, da Masu Unguwanni, da Limaman Masallatai, da kuma al’ummar garin Tsanyawa, da su ƙara himma wajen yin addu’o’i a gidajensu da kuma wuraren ibada domin neman zaman lafiya da kariyar Allah S.W.T.

Wannan na cikin sanarwar da jami'in yaɗa labarai na Ƙaramar Hukumar Tsanyawa, Yusuf Idris Isyaku ya aikowa Dala FM Kano.

Sanarwar ta ce Hakimin ya kuma buƙaci Limaman Masallatan Juma’a da su sanya addu’o’i na musamman a cikin hudubarsu, da kuma bayan sallah, tare da roƙon Allah madaukakin Sarki ya kare garin Tsanyawa da Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

‎Haka kuma, ya umarci al’ummar garin Tsanyawa da su kasance masu lura da dukkanin wani baƙon fuska da ba a sanshi ba, a rinƙa gaggauta sanar da jami’an tsaro ko shugabannin unguwa domin ɗaukar matakin da ya dace.

‎Hakimin na Tsanyawa, ya kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya kawo wa yankin zaman lafiya, da kwanciyar hankali da kuma ci gaba a garin Tsanyawa, Jihar Kano baki ɗaya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM