Rundunar ƴan sandan Kano ta cafke Muhammed Isah kan zargin safarar makamai da kayan soji zuwa ga ƴan bindiga a jihar

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke Muhammed Isah Haruna, mai shekaru 28, kan zargin sa da laifin safarar makamai da kayan soji zuwa ga ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Bichi ta jihar.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce jami’an ‘yan sanda na Bichi sun samu nasarar kama Mohammed Isah Haruna mai shekaru 28 bayan samun sahihan bayanan sirri daga wani mai kishin ƙasa da kuma haɗin gwiwar al’ummar Rimawa.
Sanarwar ta ce yayin binciken wanda ake zargin, an ƙwato mujallar bindigar AK-47 ɗauke da harsasai 30, ƙarin harsasai 79 na AK-47, kaya biyu na soji da ake zargin na bogi ne, hulunan soji guda uku.
Sauran kayayyakin sun haɗar da katin shaidar soja na bogi, da wasu katunan shaida da na banki, tare da takalman soji.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa cewa an aike shi ne domin ya kai kayayyakim da aka ƙwato ga ’yan bindiga da ke cikin daji.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Rimawa bisa sanya ido da kuma gaggauta bai wa jami’an tsaro bayanan da suka kai ga nasarar kama wanda ake zargin.
Rundunar ta ce ta fara zurfafa bincike domin kamo sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, kafin gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.



