Koma Labarai
Tsaro

Ku bai wa hukumomin tsaro haɗin kai don daƙile matsalolin tsaro a Kano - Ƴan Sanda

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ku bai wa hukumomin tsaro haɗin kai don daƙile matsalolin tsaro a Kano - Ƴan Sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta buƙaci al'umma ciki har da iyayen yara da Kwamitocin tsaro, da su bada haɗin kan da ya dace ga hukumomin tsaron, domin ganin an kawo ƙarshen matsalolin tsaro a faɗin jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu yankuna ke fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan jihar Kano, musamman ma na masu ƙwacen waya da faɗan daba da barazanar ƴan bindiga a wasu yankunan karkara.

Sai dai CSP Kiyawa ya ce, duk da ɓurbushin matsalar tsaron da ake fuskanta a wasu yankuna na jihar, amma dai Kano tana zaune lafiya, kuma akwai buƙatar al'umma su bada haɗin kai ba tare da shakku ba domin ƙara daƙile matsalolin tsaron.

Ready to PlayDala FM88.5 FM