Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama matashi Saddiƙu Yahaya ɗauke da tarin ƙwayoyi da yake sayarwa a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama matashi Saddiƙu Yahaya ɗauke da tarin ƙwayoyi da yake sayarwa a Kano

Rundunar tsaro dake yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta cafke matashi Saddiƙu Yahaya mai hannu ɗaya, bisa zargin sa da laifin dillancin ƙwayoyi a unguwar Aisami.

Rundunar tsaron ta kuma ce ta kama matashin ne a lokacin da jami'an ta suke sintiri da tala-tailin dare a unguwar ta Aisami, sakamakon bayanan sirrin da suka samu kan yadda ake hada-hadar ƙwayoyi a yankin cikin dare.

Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa ya shaidawa Dala FM Kano cewa, sun cafke matashi Sadiƙu Yahaya mai hannu ɗaya, ne da wasu tarin ƙwayoyin da ke bugarwa, waɗanda suka haɗar da Ƙwaya samfurin Fiji guda 60, da Diyaza 38 da kuma Exol guda ɗaya, da ake zargin yana sayar wa a unguwar Aisami.

Matashi Saddiƙu Yahaya da ake zargi da sayar da ƙwayoyin, ya ce wai yana sayar da su ne domin ya samu na abinci, ko da ike ya ce shi baya sha saboda ƙwayoyin sun fi ƙarfin kansa.

Sai dai matashi Saddiƙu ya bayyana nadamar sa, inda ya ce da yardar Allah daga wannan ya yi bankwana da sayar da ƙwayoyin.

Daga bisani dai Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya ce tuni ya yi umarnin a miƙa matashin inda ya dace da zarar an kammala bincike domin ganin ya girbi abinda ya shuka.

Ya kuma gargaɗi duk mutanen da ke sayar da ƙwayoyi da sauran kayan da ke bugar wa da su daina tare da neman sana'ar da ta dace, domin duk wanda ya zo hannun su da irin wannan laifi ba za su saurara masa ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM