Mahaukacin kare ya ciji mutane 18, sai dai fusatattun matasa sun kashe shi a Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa, aƙalla mutane 18 sun samu raunukan cizo daga wani kare da ake zargin ya na ɗauke da cutar hauka a wasu yankuna da ke karamar hukumar Garko ta Jihar Kano.
Hukumar kula da Dazuka ta ƙasa (NFSS), reshen ƙaramar hukumar Garko ta fara farautar karen, tare da wasu karnuka biyu da ake zargin sun kamu da cutar.
A cewar hukumar, karen ya fara kai hari tare da cizon mutane su 11 a garin Garko, kafin daga bisani ya wuce wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da garin.
Tuni dai wasu fusatattun matasa suka kashe karen bayan da ya ciji mutanen.
Hukumar ta ce wasu mutane bakwai kuma sun samu cizon karen a Raɓa, da Kadage, Gurjiya da kuma Dausai, lamarin da ya sa adadin waɗanda aka ruwaito sun ji rauni ya kai kimanin mutane 18.
Hukumar NFSS ta tura jami'anta zuwa yankunan da lamarin ya shafa, domin gano karnukan da ake zargin sun kamu da cutar tare da daƙile ci gaba da kai hare-haren ga mutane, kamar yadda kafar Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar ta kuma buƙaci mazauna Garko da sauran yankunan da ke kusa, da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da kai rahoton karnukan da suka ɓata ko kuma dabbobin da ke nuna alamun cutar hauka ga hukumomin da abin ya shafa.
Kazalika, Hukumar ta shawarci duk wanda kare ya cije shi ko kuma ya yi mu'amala da dabbar da ake zargin tana dauke da cutar da ya garzaya asibiti domin samun kulawar likita cikin gaggawa.



