Koma Labarai
Tsaro

Rundunar soji na neman jami'in ta ruwa a jallo bisa zargin sayar wa yan ta'adda kaki a Najeriya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar soji na neman jami'in ta ruwa a jallo bisa zargin sayar wa yan ta'adda kaki a Najeriya

Rundunar sojoji ta Nigerian Army Ordnance Corps (NAOC) ta ayyana wani jami'inta mai suna Mohammed Yusuf Amutu, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da sayar da kayan sojoji, musamman kakin soja, ga 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka.

Wannan na cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Oluwatope Aluko, ya fitar a ranar Alhamis 23 ga Yuli, 2026.

Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa Amutu, wanda ke aiki a kamfanin samar da kakin soja na Nigerian Army Ordnance Kits Factory, ya tsere daga sansaninsa tun a ranar 3 ga Yuni, 2026.

Kazalika Sanarwar ta kuma ce, hukumomin soja sun ayyana shi a matsayin wanda ake nema, tare da ƙaddamar da bincike da farautar sa domin kama shi da gurfanar da shi bisa dokokin soja, kamar yadda kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Haka kuma, Rundunar ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau'in rashin ɗa'a ko halin da zai iya kawo cikas ga ayyukan tsaro ko barazana ga tsaron ƙasa ba.

Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani jami'in da aka samu da hannu wajen sayarwa, ko karkatarwa ko bai wa 'yan ta'adda da masu laifi kayan sojoji ba tare da izini ba, zai fuskanci hukunci mai tsauri bisa dokokin soja da na farar hula.

Ta buƙaci al'umma su bai wa jami'an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen cafke wanda ake nema, tana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin sa ido da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Ready to PlayDala FM88.5 FM