Jami'an Bijilante 6,700 ne za su yi aikin samar da tsaro yayin bikin Babbar Sallah a Kano - Shehu Rabi'u

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta jihar Kano, ta bayyana cewa sama da jami'an ta dubu 6,700, ne za su yi aiki a cikin farin kaya da masu sanye da kayan sarki, domin tabbatar da tsaro da kare rayukan al'umma yayin bikin Babbar Sallah.
Babban Kwamandan ƙungiyar a Kano, Shehu Muhammad Rabi'u, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai, a wani ɓangare na shirye-shiryen su na tunkarar bukukuwan Babbar Sallah, domin wanzar da tsaron rayuka da dukiyoyin Al'ummar jihar.
Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa Shehu Rabi'u ya kuma buƙaci iyaye musamman ma Mata, da su kiyaye wajen kula da yara a yayin ziyarar Dangi da guraren bukukuwan Sallah don gudun batan yara a yayin bikin Sallar.
Har ila yau, ya yi kira ga daukacin al'umma da su kasance masu bayar da bayanan sirri da zarar sun ga wani motsin abinda ba su yarda da shi ba, domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.
A ranar Laraba 27 ga Mayu, 2026, ne dai za a gudanar da bikin Babbar Sallah, a faɗin duniya, yayin da kuma ɗumbin al'umma ke gudanar da tsayuwar Arfa a wani ɓangare na aikin Hajjin bana, yau Talata a ƙasa mai tsarki.



