Gwamnatin Kano ta gargaɗi masu ƙona tayoyi da sunan babbaka a lokacin sallah

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi al’umma da su ƙauracewa ƙona tayoyi da sunan babbaka, wanda hakan ke gurbata yanayi musamman a wannan lokacin na bukukwan babbar sallah.
Wannan na ƙunshe ne a cikin a wata sanarwa da muƙaddashin daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi na Kano, Malam Nasiru Musa Aliko ya fitar ga manema labarai.
Ya ce akwai dokar yana kona tayoyi a jihar nan, wanda dokar tayi tanadin hukunta duk wanda aka samu da laifin kona tayoyin a ko wane lokaci.
Malam Nasiru Musa Aliko ya ƙara da cewa, kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi na Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim yayi kira ga al’ummar jihar nan, dasu binne jini da kuma saura dagwalon dabbobin da aka yanka.
Daga bisani sanarwar tace ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta Kano ta janye aikin tsaftar muhalli na ranar Asabar sakamakon bukukuwan sallah babba.



