Koma Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta yi haɗin gwiwa da NDLEA, don ƙara daƙile shan miyagun ƙwayoyi da dillancin su a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta yi haɗin gwiwa da NDLEA, don ƙara daƙile shan miyagun ƙwayoyi da dillancin su a Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano ƙarkashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta ziyarci hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, domin ƙulla alaƙar aiki, da kuma tattauna batun yadda za a ƙara daƙile ta'ammali da kayan maye a jihar.

Hukumar ta kai ziyarar ne a ranar Juma'a 9 ga watan Oktoba, 2026, inda tawagar ta gana da Kwamandan hukumar NDLEA, na Kano, Ɗahiru Yahaya Lawal, da sauran jami'an sa.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce ziyarar na da nufin haɗa kai da hukumar NDLEA, domin ganin an ƙara kawo ƙarshen sha da dillancin kayan maye a faɗin jihar.

Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma yaba da irin ƙoƙarin Kwamandan hukumar NDLEA, na Kano, Ɗahiru Yahaya Lawal, bisa yadda yake taka rawa wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da sauran kayan shaye-shaye.

Shima a nasa ɓangaren, Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, Ɗahiru Yahaya Lawal, ya yaba da ziyarar da hukumar shari'ar ta kai musu.

Ya kuma ce akwai buƙatar limamai su ƙara himma wajen faɗakar da al'umma kan illar ta'ammali da kayan maye yayin huɗubobin su na Juma'a a kan mumbari.

A nasa jawabin, Kwamishina na ɗaya a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Gwani Muhammad Tahir Yakasai, ya buƙaci iyaye da su ƙara tsawatarwa da ƴaƴansu kan illar shan kayan maye, bisa yadda suke da illa ga rayuwar su.

A yayin ziyarar, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya jagoranci sallar juma'a a hukumar, daga bisani kuma hukumar NDLEA, ta zagaya da su ɗakunan da aka ajiye waɗanda ake zargi da ta'ammali da kayan maye inda ta yi musu nasihohi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM