Zainab Musa Kwankwaso ta saku, Inji Malam Ibrahim Khalil
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Malam Ibrahim Khalil ya bayyana cewa, Hajiya Zainab Musa Kwankwaso ta saku daga auren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa mijin nata ya furta kalmar saki ne cikin nishaɗi, ba cikin fushi ba.
Rahama Radio ta wallafa cewa, malamin ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan batun auren ma’auratan, inda ya gargaɗi al’umma da su guji katsalandan a harkokin aure tsakanin mata da mazajensu.
Haka kuma, Malam Ibrahim Khalil ya buƙaci a bai wa malamai damar shiga tsakani domin ƙoƙarin sasanta ma’auratan, idan har akwai yiwuwar sulhu a tsakaninsu.
Malamin ya kuma ja hankalin al’umma da su guji siyasantar da batun auren.



