NUT ta shiga yajin aiki kan sace ɗalibai da malamai a jihar Oyo

Ƙungiyar Malamai ta Nijeriya NUT, reshen jihar Oyo, ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a jihar, tare da sanar da shirinta na gudanar da gangamin nuna goyon baya a faɗin ƙasar domin matsa wa gwamnati lamba ta kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
Yajin aikin ya fara ne daga ranar Litinin, 1 ga Yunin 2026, saboda gazawar da suka ce an yi wajen ganin an sako waɗanda aka sace, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cikin wata takarda da shugaban ƙungiyar na ƙasa Audu Amba, da babban sakatarenta, Clinton J. Ikpitibo, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana matuƙar damuwarta kan abin da ta kira mummunan yanayi mai firgitarwa da kuma raɗaɗin da waɗanda aka sace ke fuskanta a yayin da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Sai dai tuni shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bayar da umarnin girke jami’an tsaron gandun daji 1,000 a jihar Oyo.
Har ila yau, ya kuma umarci wata rundunar tsaro ta musamman da ta ƙara ƙaimi wajen kubutar da ɗalibai da malaman da aka sace daga makarantu uku da ke karamar hukumar Oriire.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya sanya wa hannu ranar Lahadi, ta ce wata babbar tawagar gwamnatin tarayya ta isar da umarnin shugaban ƙasar ga shugabannin al’umma da ’yan majalisa yayin wata ziyara da suka kai wa al’ummomin Esiele da Yawota da ke karamar hukumar Oriire a ranar 31 ga Mayun 2026.



