Hukumar NASENI, ta tallafa wa mutane 1,000, da kayan girki da shinkafa a ƙaramar hukumar Kabo, Kano.

Hukumar Kula da Ingancin Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa, NASENI, ta ƙaddamar da rabon kayan tallafi da suka haɗa da murhunan girki na zamani, da buhunan shinkafa ga mutane 1,000, a Ƙaramar Hukumar Kabo ta Jihar Kano.
Hukumar ta ce matakin na da nufin rage wa al’umma raɗaɗi da kuma tallafa wa mata wajen gudanar da harkokin yau da kullum.
Da yake ƙaddamar da rabon kayan, Shugaban NASENI, Alhaji Khalil Sulaiman Halilu, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne musamman domin tallafa wa mata da kayan girki, da nufin rage musu wahala da inganta rayuwarsu.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Hon. Lawal Najume, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka tuna da al’ummar yankin tare da tallafa musu.
Taron ya samu halartar Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Ƙungiyoyi, Shugaban Ma’aikata a Fadar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, da Hakimin Kabo, Alhaji Bashir Ado Bayero, da sauran masu ruwa da tsaki.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Hukumar NASENI ta ce mutane dubu ɗaya ne suka amfana da tallafin, inda ta bayyana cewa kayan da aka rabon an samar da su ne a cikin gida Najeriya.



