Koma Labarai
Labarai

Mun yi mamaki da Majalisar Dokokin Kano ta ce za ta binciki dillalai amma ba ta tuntuɓe mu ba - Ƙungiyar KPADA

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mun yi mamaki da Majalisar Dokokin Kano ta ce za ta binciki dillalai amma ba ta tuntuɓe mu ba - Ƙungiyar KPADA

Kungiyar masu sayar da filaye da gidaje da bada hayar su ta jihar Kano, KPADA, ta ce ta hanyar samar da doka da tsari daga bangaren gwamnatin jihar Kano ne za a magance matsalolin da ake fuskanta a harkokin dillancin gidaje da filaye, da ma magance matsalar tsaron da ake fuskanta ta bangaren a jihar.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Shugaban ƙungiyar ta KPADA, Alhaji Isah Jibril Isah ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Alhamis 23 ga Yuli, 2026.

Kaci ƙasa na wannan jawabin ne bayan da Majalisar ta ce za ta soma bincike kan zargin dillalan gidaje da filaye da masu ba da gidajen haya da karɓar kuɗaɗen da suka wuce ƙima daga jama’a a jihar.

Sai dai Alhaji Jibril Kaci ƙasa ya ce, akwai abin ban mamaki kan yadda majalisar ta ɗauki gaɓarar gudanar da bincike a kan dillalan amma ba tare da ta tintuɓe mu ba kasancewar su ne suka san hanyoyin da ya kamata abi domin magance wannan matsala da ake magana akai.

A cewar sa, "Mun daɗe mu na kiraye-kiraye ga gwamnatin jihar Kano, da Majalisar da ma dukkan masu ruwa da tsaki wajen ganin an ɗauki matakin da ya dace domin ƙara kawo tsafta a cikin harkar bada haya, da sayar da gidaje da filaye, amma shiru ba a yi komai akai ba," in ji shi.

Alhaji Isah Jibril, ya ce kuma ce matuƙar da gaske gyaran za a yi a wannan ɓangare babu makawa sai an yi zama na musamman da masu harkar ƙasa da gidaje an karɓi koken su, tare da samar da tsayayyiyar doka da tsari.

Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin Kano ta samar da hukuma da za ta rinƙa tabbatar da an bi doka a harkokin gidaje da ƙasa, domin ganin an daƙile matsalolin da ake fuskanta, tare da daƙile matsalar tsaron da ake fuskanta a ɓangaren.

Ready to PlayDala FM88.5 FM