Uwa da ɗan ta, da wani mutum sun rasa ransu dalilin faɗawa Rijiya a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wani mutum, da ba a gano sunan sa ba, sakamakon faɗawar da cikin Rijiya a unguwar Samegu daura da gida burodin El-Sadeq, da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a yammacin Juma'a 29 ga Mayu, 2026.
Ya ce sun samu kiran gaggawa ne daga wani mutum mai suna Hafizu Garba Saminu, inda ya sanar da faɗawar mutumin a cikin rijiyar, inda da zuwan jami'an su suka ciro mutumin, daga baya aka tabbatar da rasuwar sa.
Sanarwar ta kuma ce, daga bisani jami'an hukumar sun miƙa gawar mutumin a hannun jami'in rundunar Ƴan Sanda, mai muƙamin DCO, a ofishin ƴan sanda na Fanshekara mai suna Salisu Salihu.
Har ila yau, ACFO Saminu Yusuf, ya kuma ce, jami'an nasu sun kuma ciro wata mata mai shekaru 32, bayan da ta faɗa Rijiya, a Ƙauyen Madarin Taba, tare da Ɗanta ɗan kimanin wata 18, Mai suna Harisu Muntari.
A cewar sa, bayan an ciro matar wadda ke da taɓin Ƙwaƙwalwa, da ɗan nata daga cikin rijiyar an tarar dukka Allah ya yi musu rasuwa, a nan ne aka miƙa su hannu mai unguwar Yusuf Suraja, da mahaifinta Muhammad Shitu.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Saminu Yusuf ya kuma ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin faɗawar su cikin rijiyar.
Sanarwar ta ce, Daraktan Hukumar kashe gobarar a jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya ja hankalin masu gidaje musamman ma iyaye, da su tabbata suna rufe rijiyoyin da ke gidajen su da murafe, domin kaucewa faruwar irin Iftila'in da ya faru.
