Koma Labarai
Iftila'i

Matashi ya rasu a gidan budurwarsa ƴar Tik-tok a unguwar Ɗanbare da ke Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Matashi ya rasu a gidan budurwarsa ƴar Tik-tok a unguwar Ɗanbare da ke Kano

Yanzu haka an yi jana’izar matashi Isma’il Makaye, wanda ke sana’ar sayar da kayan kwalliya, bayan rasuwarsa a wani yanayi mai cike da ruɗani a gidan wata fitacciyar ƴar TikTok da ake kira Fati Cele a Kano.

Wasu majiyoyi sun shaida cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a 19 ga Yuni, 2026, inda aka ce Fati Cele ta fito daga gidanta tana neman taimako bayan gano abin da ya faru.

Bayan shiga cikin gidan ne, aka tarar da marigayin cikin wani hali da ya jawo tambayoyi daga jama’a.

Wani makusancin marigayin ya bayyana cewa an garzaya da matashin zuwa Asibitin Nassarawa domin ceto rayuwarsa, sai dai daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa, kafin a yi jana’izarsa a Unguwa Uku Yan Awaki.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga ofishin Ɗorayi Babba sun fara bincike kan lamarin tare da tsare wata da ake zargi domin taimakawa bincike.

Majiyoyi sun ce marigayin da wadda ake bincike a kanta sun taɓa samun saɓani a tsakanin su a baya, amma daga bisani sun sasanta dangantakarsu, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM