Wata mota ta faɗo daga saman Gadar Dangi a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa an samu hatsarin mota a ƙasan gadar Shataletalen Dangi da ke birnin Kano a safiyar yau Talata, bayan da wata mota ta kife lokacin da take tafiya a kan hanyar.
Lamarin ya janyo cunkoson ababen hawa na ɗan lokaci, inda masu amfani da hanyar suka fuskanci tsaiko sakamakon yadda motar ta toshe wani ɓangare na titin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin hatsarin ba, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan abin da ya haddasa lamarin.
Haka kuma, ba a samu cikakken bayani kan ko akwai asarar rayuka ko kuma waɗanda suka jikkata ba.
Rahotanni sun bayyana cewa direban motar ya samu raunuka bayan da motarsa ta kwace masa tare da kifewa a Gadar Dangi da ke kan titin Zariya a Jihar Kano.
Wani shaidar gani da ido, ya shaida wa Arewa Radio Kano, cewa motar ta bugi gadar ne bayan direban ya rasa iko da ita, kafin daga bisani ta bugi wata mota da ke kan gadar, lamarin da ya sa ɗaya daga cikin tayoyin gaban motar ta fashe.
Shaidar ya ce direban ya samu rauni a kai, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa.



