Ƙungiyar PUTCCM, ta gudanar da gangamin wayar da kan jama'a kan muhimmancin zaɓe a Kano.

Ƙungiyar wayar da kan al'umma kan mahimmancin zaɓe da kare ƙuri'u a yayin zaɓe, ta PUTCCM, ta buƙaci hukumar zaɓe ta ƙasa da ta tabbata an yi adalci a zaɓen da ke tafe na 2027.
Ƙungiyar ta buƙaci hakan ne a yayin wani gangamin wayar da jama'a kan mahimmancin yin zaɓe da ta gudanar ranar Talata, a jihar Kano, a dai-dai lokacin da babban zaɓen 2027, ke ƙara gabatowa.
Da yake ƙarin bayani, Ko-odinatan Ƙungiyar ta PUTCCM a Kano, Isah Garba, wanda akafi sani da Ɗan Aljannah, ya ce sun gudanar da gangamin ne domin wayar da kan jama'a kan muhimmancin yin zaɓe, da ma yadda ya kamata al'umma su kare ƙuri'un su bayan kaɗa zaɓe.
Isah Garba ya kuma ce ya zama wajibi hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar da adalci a yayin zaɓen 2027, tare da yin duk mai yiyuwa wajen ganin an kare ƙuri'un masu zaɓe an kuma yi adalci da gaskiya a yayin sanar da sakamakon zaɓe.
Mallam Rabi'u Lambu shi ne mataimakin Ko-odinatan Ƙungiyar ta PUTCCM a Kano, ya buƙaci al'umma da su kasance masu bin doka da oda a yayin zaɓen 2027, tare da kafawa su tsare don ganin an tabbatar da adalci.
A yayin gangamin dai, Ƴan ƙungiyar ta PUTCCM, sun zagaya yankuna daban daban na jihar Kano, kuma ciki har da yankunan Sabon gari, inda suka ɗunguma zuwa ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, reshen jihar Kano, domin wayar da kan jama'a, tare da miƙat buƙatar su ga hukumar ta tabbatar an yi adalci a zaɓen 2027.



