Hukumar Hisbah ta haramta sana'ar tura fina-finai wato (Downloading" a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta sana'ar tura fina-finai wato "Downloading" a faɗin jihar, bisa zargin amfani da sana'ar wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa doka da tarbiyya a jihar.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM a ranar Laraba 15 ga Yuli, 2026.
Ya ce hukumar ta lura da yadda masu tura fina-finan suke amfani da sana'ar wajen tura wa yara da matasa fina-finan da basu dace ba na batsa da sauran bidiyon da bai dace yara su kalla ba domin za su ɓata musu tarbiyya.
Dr. Mujahideen ya kuma ƙara da cewa, yanzu haka jami'an su za su fara zagaya wa ƙananan hukumomin jihar Kano 44, domin tabbatar da masu tura fina-finan sun bi dokar yadda ya dace.
A cewar sa, "Duk wanda muka kama da bijirewa wannan doka hukumar mu za ta gurfanar da shi a gaban kotu domin girbar abinda ya shuka," in ji shi.



