Koma Labarai
Labarai

Adeleke ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Osun karo na biyu.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Adeleke ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Osun karo na biyu.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta ayyana Ademola Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam'iyar Accord, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ademola Adeleke dai ya samu ƙuri’u 511,067, yayin da Oyebamiji na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 444,815.

Ya samu nasarar ne a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30, yayin da Oyebamiji na APC ya lashe guda 11.

Wannan nasara ta ba Adeleke damar komawa kujerar gwamnan Osun na wa’adi na biyu.

A ranar Asabar 15 ga watan Agusta, 2026, ne dai aka gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.

Ready to PlayDala FM88.5 FM