Koma Labarai
Labarai

Fitaccen mawakin siyasa Ƙosan Waƙa ya rasu

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Fitaccen mawakin siyasa Ƙosan Waƙa ya rasu

Allah ya yi wa fitaccen mawaƙin siyasar nan Muhammad Buhari, wanda aka fi sani da Ƙosan Waƙa rasuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa Marigayi Ƙosan Waƙa ya rasu ne yau, biyo bayan shan fama da rashin lafiya a asibiti.

Marigayin kafin rasuwar sa ya yi fice a sha'anin wakoƙin siyasa, wanda shi ne ma ya yi waƙar "Abba Ka Cika Gwarzo, komai ake buƙata ka yi" da dai sauransu.

Yanzu haka dai al'umma da dama ne ke ci gaba da bayyana alhinin su kan rasuwar Ƙosan Waƙa.

Mu na tafe da ƙarin bayani a kan rasuwar marigayi Ƙosan Waƙa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM