Koma Labarai
Labarai

REMASAB, ta kwashe kayan aikin ginin da wasu suka zuba a kan titunan Farm Center, Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
REMASAB, ta kwashe kayan aikin ginin da wasu suka zuba a kan titunan Farm Center, Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Kwashe Shara ta Kano REMASAB, ta kwashe kayan ginin da wasu suka zuba a kan titunan Farm Centre da ke birnin jihar Kano.

Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran REMASAB, Abubakar Ahmad, ya fitar a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026.

A cewar Sanarwar, Kwamitin Karta-Kwana na hukumar ne ya gudanar da aikin a daren Laraba, 16 ga Satumba, 2026, inda ya kwashe tarin kayan ginin da aka zuba a kan Titin Guda Abdullahi da Titin Marhaba Cinema.

Sanarwar ta kuma ce, aikin ya biyo bayan rahoton da hukumar ta ce ta samu daga wasu mazauna yankin, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.

Shugaban Hukumar, Dr. Muhammad Salisu Khalil, ya ce REMASAB za ta ɗauki duk wani kayan gini da aka zuba a kan titi ko wuraren da bai dace ba, a matsayin shara tare da kwashe shi nan take.

Dr. Muhammad ya ƙara da cewa, zuba bulo, dutse, yashi ko kwaɓa siminti a kan tituna da magudanan ruwa na iya kawo cikas ga zirga-zirga da hanyoyin ruwa.

Dr. Khalil ya buƙaci masu ajiye kayan gini a kan tituna su gaggauta kwashe su, tare da cewa waɗanda suka ci gaba da amfani da titunan jama’a wajen ajiye kayan gini za su fuskanci matakan da suka dace bisa dokokin muhalli.

Har ila yau, ya kuma buƙaci jama’a da su kai wa hukumar rahoton wuraren da ake zuba kayan gini ko amfani da tituna da magudanan ruwa ba bisa ƙa’ida ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM