Koma Labarai
Tsaro

Masu faɗan daba sun yi sanadiyyar rasuwar matashi Yusuf Ahmad a unguwar Ɗorayi, Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Masu faɗan daba sun yi sanadiyyar rasuwar matashi Yusuf Ahmad a unguwar Ɗorayi, Kano.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana kama wasu matasa da ake zargi da hannu a kan kashe wani matashi Yusuf Ahmad, ta hanyar saransa a Ƙirji da wuya, a tsallaken unguwar Ɗorayi ƙonannen gidan Mai a cikin daren jiya Talata.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani bidiyo na kai tsaye, da ya yi a shafin sa na Facebook, a yankin Ɗorayi Ƙonannen gidan mai, lokacin da rukunin jami'an tsaro suka isa yankin.

A cewar sa, "Rundunar mu ta samu kiran gaggawa kan faɗan, inda Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin tura jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru domin kai ɗauki," in ji shi.

CSP Kiyawa ya kuma ce, bayanan farko sun nuna cewa wasu matasa sun yi wa ɗan wani tsallake a unguwar Ɗorayi ƙonannen gidan Mai, rauni, abin da ya fusata ’yan yankinsa, inda su ma suka yo gayya suka fito domin ɗaukar fansa.

Kiyawa ya ƙara da cewa, ’yan sanda sun kai ɗauki a cikin daren tare da kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin waɗanda ya ce za a wuce da su Hedikwatar rundunar da ke unguwar Bompai a Kano.

Wata majiya ta shaidawa Dala FM Kano cewa, matashin da aka kashe ba ya faɗan daba, kawai dai akwai wani yayan sa da ya yi harkar a baya, amma yanzu ya daina, kuma yana daga cikin masu bada gudunmawa wajen yaƙi da faɗan dabar a Ɗorayi.

Wani mazaunin yankin, Salihu Shamsu Saleh, ya bayyana wa Arewa Update cewa, Yusuf ya je maulidin makarantarsu tsallaken, kuma a kan hanyarsa ne masu faɗan dabar suka afka masa, inda ya ce an sare shi a ƙirji da wuya.

Shi ma wani mazaunin yankin, mai suna Aminu Maifulo Dorayi, ya ja hankalin matasan Dorayi da su guji faɗan daba da ɗaukar doka a hannu, yana mai kira gare su da su kai saɓanin da ya taso ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma da hukumomin tsaro.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Kiyawa, ya jaddada cewa, ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a kan kitsa lamarin don ɗaukar mataki na gaba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM