A dawo min da dukiya ta tunda an hana ni auren - Lauya a Kano

Babbar kotun shari'ar Muslunci mai zaman ta a Ɗanbare ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halhalatul Kuza'I Zakariyya, ta sanya ranar 27 ga watan Satumba, 2026, domin ci gaba da sauraron wata Shari'a wadda wani lauya mai suna Usman Isma'il ya shigar.
Lauyan yana ƙarar Binta mai kaji Fagge da Amina Usman Musa Fagge, da kuma Alhaji Aminu Sarki, bisa da'awar a dawo masa da dukiyar aure da ya nema na Amina a ƙarshe aka hana shi auren.
A zaman kotun na yau, lauyan mai ƙara Muhammad Sani Bello, ya gabatar da wata takarda mai ɗauke da lissafin kayayyaki na kusan Naira miliyan shida.
Lauyan ya roƙi Kotun da ta bada umarnin a dawo masa da dukiyar sa tunda an hana shi auren.
Kotun ta bayyana cewar ya dauki hoton takaddar ya bawa kotun ya kuma bawa wadanda ake kara domin su yi nazari.
Kotun ta sanya ranar 27 ga watan gobe domin jin martanin waɗanda ake ƙara.



