Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta amince da biyan alawus ga likitoci 90 a jihar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta amince da biyan alawus ga likitoci 90 a jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan alawus ga likitoci 90 da suka cancanta, tare da fara shirye-shiryen daidaita tsarin albashin likitocin jihar da na Gwamnatin Tarayya.

Hakan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta fitar a ranar Juma'a 23 ga watan Oktoba, 2026

Kafar Arewa update ta ruwaito cewa, Samira ta ce, matakin ya biyo bayan shirin yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ƙungiyar likitoci ta NAGGMDP ta sanar, sakamakon wasu buƙatu da suka shafi haƙƙoƙin ma’aikatanta.

Gwamnatin ta kuma fara lissafin alawus na ma’aikatan lafiya da ke aiki a yankunan karkara, tare da bayyana cewa za a bi matakan gudanarwa domin tabbatar da biyan waɗanda suka cancanta.

Sanarwar ta kuma buƙaci ƙungiyar likitocin ta ci gaba da tattaunawa da hukumomi tare da ba da damar kammala matakan da aka fara, domin kauce wa katse ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM